Sabon gwamnan Zamfara ya bawa tsohon ministan Jonathan mukami


Legit Hausa

Sabon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya nada tsohon Ministan Kudi a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, Bashir Yuguda a matsayin mai bashi shawara na musamman. Gwamnan ya yiwa Yuguda nadin ne tare da wasu mutane shida kamar yadda ya ke dauke cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ayyuka da nade-naden 'yan fadan gwamnati na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ibrahim Suleiman.

Sauran da aka yiwa nadin mukamman sun hada da sabon sakataren gwamnati, (SSG) Alhaji Bala Bello, Babban mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tsaro(SSA)Alhaji Abubakar Dauran da Alhaji Bello Ibrahim a matsayin SSA kan sabuwar kafar yada labarai. 

Sauran sun hada da Alhaji Umar Sani Mataimaki na musamman kan tsare-tsare, Alhaji Kabiru Yusuf, Direkta Janar kan harkokin tsare-tsare da Alhaji Saidu Maishanu mai'aikacin FRCN Pride FM a matsayin Babban Manajan Hukumar Kula da Gidan Rediyo da Talabijin na Zamfara (ZRTV). Sanarwar ta aka fitar a yammacin ranar Juma'a ta ce dukkan wadanda aka yiwa nadin za su kama aiki nan ta ke.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN