Sabbin ministoci: Baraka na kokarin kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu


Legit Hausa

Ana kyautata zaton cewar tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, zai samu gurbin minista daga jihar Legas a cikin majalisar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kafa. Shugabancin jam'iyyar ne ya bawa shugaban kasa shawarar bayar da mukamin minista ga dukkan gwamnonin APC da basu samu koma wa a zango na biyu ba.

Bisa wannan shawara ta uwar jam'yyar APC, ana kyautata zaton cewar Ambode, Mohammed Bindow (tsohon gwamnan jihar Adamawa) da Mohammed Abubakar (tsohon gwamnan jihar Bauchi), zasu samu mukamin minista. Saidai, Ambode na fuskantar babban kalubale daga wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC da suka hana shi samun tikitin takarar gwamna a karo na biyu.

Sakataren tsare-tsaren jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Ahmed Lawan, ya tabbatar da cewar mai yiwuwa Bindow ya samu mukamin minista kamar yadda wata majiya ta tabbatar da cewar masu ido da kwalli a fadar shugaban kasa sun bayyana cewar Ambode zai iya samun mukamin minista duk da ya gaza cin zaben cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Legas. Amma wata kungiya (Mandate Group) da ke biyayya ga jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ta ci damarar ganin ta kara daukan fansa a kan Ambode kamar yadda ta yi masa a jihar Legas.

Kungiyar ta yaki Ambode a Legas tare da kafa danlelen Tinubu, Babajide Sanwa-Olu, a kujerar gwamnan jihar. Rahotanni sun bayyana cewar babban zunubin Ambode shine kwace kwangiloli daga hannun kamfanonin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Legas tare da bawa kamfanonin da ake zargin yana da hannun jari a cikinsu. Saidai duk da kokarin da kungiyar Tinubu ke yi na ganin Ambode bai samu kujerar minista ba, fadar shugaban kasa na nuna alamun ba zata ajiye shi ba. Lamarin da ake ganin zai haifar da baraka a tsakanin shugaba Buhari da Tinubu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN