• Labaran yau

  Rikicin APC na kara zurfi yayinda Gwamnoni ke shirin sauya Oshiomhole


  Legit Hausa

  Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, na a cikin tsaka mai wuya yayinda ake ta kulla-kullan ganin an tsige shi daga kan kujerarsa. Jaridar Tribune ta ruwaito cewa akwai sabon yunkuri da ake na ganin an fitar da shi daga sakatariyar jam’iyyar na kasa yayinda yake shiri cika shekara guda akan kujerar shugabancin jam’iyyar.

  Wata majiya ta jam’iyyar ta bayyana cewa gwamnoin APC sun gabatar da wata bukata na son chanjin Shugaban jam’iyyar yayinda suka gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a mako da ya gabata. Gwamnan jihar Kebbi kuma Shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Abubakar Atiku Baudu ya jagoranci takwarorinsa zuwa wajeen ganawar.

  An tattaro cewa gwamnonin APC a wajen ganawar da Buhari, sun nuna damuwa kan rikici shugabanci da ke wakana a sakatariyar jam’iyyar na kasa sannan suka roike shi kan ya sanya baki. Majiyar ta bayyana cewa da yiwuwa za a gudanar da wani taro a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a kasa da kwamitin iyayen jam’iyya domin tattauna rikicin da ke tsakanin Oshiomhole da mataimakinsa.

  Majiyar ta kuma bayyana cewar gwamnonin na duba wanda zai maye gurbin tsohon gwamnan na Edo a bayan Shugaban kasar. Sai dai an nemi jin tab akin babban sakataren labaran jam’iyyar, Mallam Lanre Isa-Onilu, amma ba a same shi ba. A nashi bangaren mataimakin kakakin jam’iyyar, Yakeen Nabena ya bayyana a wayar tarho cewa bai da labarin kowani shiri na kiran taro asu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rikicin APC na kara zurfi yayinda Gwamnoni ke shirin sauya Oshiomhole Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });