Ribar da yankin arewa ya samu a karkashi mulkin Buhari

Legit Hausa
Tun bayan hawansa mulki a zango na farko, a shekarar 2015, wasu jama'a, musamman daga yankin arewacin Najeriya, suka fara korafin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fi karkata bangaren kudu, musamman yankin 'yan kabilar Yoruba, wajen shimfida aiyuka raya kasa.
Masu irin wannan ra'ayi ba su tsaya a kan batun aiyuka ba kadai, hatta a bangaren rabon manyan mukamai, sun zargi shugaba Buhari da bayar da manyan mukamai masu maiko ga yankin kudu maso yamma na 'yan kabilar Yoruba.
Hakan ne ya saka wasu masu nazarin al'amuran siyasa da aiyukan gwamnatin shugaba Buhari suka fitar da jerin wasu aiyukan da Buhari ya yi a yankin arewa domin ya zama raddi ga masu sukarsa a kan cewa ya y watsi da al'amuran yankinsa.
1. Aikin hanya mafi tsawo kuma mafi girma a Nijeriya da gwamnatin Buhari take yi a Arewa ne, yana da nisan sama da kilometer dari 450, shine daga Kano, Zaria, Kaduna zuwa Abuja.
2. Aikin tashar wutar Lantarki mafi girma a tarihin Nijeriya da gwamnatin shugaba Buhari take yi a Arewa ne, shine Manbilla hydro power station, idan an kammala zai samar da wuta megawatts dubu 3050.
3. Aikin bincike da hako man fetir a jihohin arewa da suka hada da Bauchi, Benuwe da Maiduguri
4. Tashar jiragen ruwa na farko a tarihin Arewa shugaba Buhari ne, itace Baro sea port, jihar Neja
5. Gwamnatin Buhari ta cigaba da iikin hanyar Kano zuwa Katsina da kuma aikin hanyar 'Bye pass' na Kano.
6. Hanyar Kano, Bauchi, Potiskum, har Borno, Arewa ne.
7. An mayar da filin jirgin saman Malam Aminu Kano terminal, irin na kasashen Turai, duk a gwamnatin Buhari, kuma a Arewa.
8. An gina Army University a Biu jihar Borno har an fara karatu, Buhari ne, Arewa ne.
9. Ya kammala aikin tashar samar da wutan Lantarki na Kashimbila, jihar Taraba.
10. Yana gina tashar wutan Lantarki da aka watsar da aikin ta shekaru 29 a Zungeru jihar Neja, yanzu an kai kashi 78 na kammalawa. Sannan ga aikin titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano ana kan yi, kuma duk aikin Buhari ne.
11. Ya kammala jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, Buhari ne, kuma Arewa ne.
12. Ya gina Air Force base mai girma, har da babban Asibitin sojojin a Bauchi, Buhari ne, Arewa ne.
13. Arewa ta ci moriyar shirin bayar da tallafi ga matasa (N-power) da ciyar da yara 'yan makarantun firamare a wadanda gwamnatin Buhari ce ta kirkire su.
14. Shugaban sojojin sama, da na kasa, da babban sifeton rundunar 'yan sanda, da babban darektan hukumar DSS, da shugaban hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), da shugabannin hukumomin FERMA da NITDA duk ‘yan Arewa Buhari ya bawa. Kazalika, ya bawa 'yan arewa Ministan tsaro, Ministar kudi da Ministan ilimi.
15. Kaso 76% na tallafin noma da gwamnatin tarayya take bayarwa, Arewa ce ke cin moriyarsa
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN