Legit Hausa
Labarin wata mata 'yar Najeriya na ta yawo a shafukan yada
zumunta na zamani, bayan da ta bayyana cewa ta mutu sannan kuma ta dawo duniya
bayan wasu kwanaki.
Mhiz Gold Abi, 'yar Najeriya ce da take zaune a Casablanca,
birnin kasar Morocco, an bayar da rahoton cewa ta mutu, inda abokanan ta suka
yi ta mamakin labarin. Wasu daga cikinsu sunyi ta jajen mutuwarta a shafukan
sada zumunta. Bayan wasu 'yan kwanaki kuma sai ta hau shafinta na sada zumunta
na Facebook ta bayyana cewa ta dawo duniya.
A matsayin ta na wacce ta mutu ta dawo, wacce ta ga lahira,
ta bayyanawa abokanan ta na Facebook cewa lahira babu dadi ko kadan, inda ta
rubuta cikin harshen turanci kamar haka "Heaven no easy oo." Sannan
tayi alkawarin bayyana irin abubuwan da ta gano a lahira, da irin abubuwan da
suka faru da ita lokacin da take lahira.
Abokanan ta wadanda suka maida mata martani a labarin da ta
rubuta din, sun bayyana jin dadinsu da ta dawo, sannan kuma sun yiwa Allah
godiya da ya bata dama a karo na biyu.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI