Rashin wutar lantarki ya hana tattalin arzikin Najeriya bunkasa - Dangote

Legit Hausa
Fittacen attajirin nan da ya yiwa duk wani bakar fata fintinkau da kuma zarra ta fuskar dukumar dukiya a fadin duniya, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana umul aba-isin da ya hana bunkasar tattalin arziki a Najeriya.
Hamshakin attajirin da ke kan sahu na gaba a nahiyyar Afirka ta fuskar tarin arziki, ya ce kasar Najeriya ba za ta taba samun ci gaba ba ta hanyar bunkasar tattalin arziki muddin aka dawwama cikin karanci da kuma rashi na wutar lantarki.
Mamallakin gidauniyar nan ta Dangote Foundation, ya ce a yayin da tattalin arziki ya zamto tubalin ci gaba na kowace kasa a fadin duniya, Najeriya ba za ta taba kai wa wannan munzali ba a sakamakon rashin wadatuwa da wutar lantarki.
Kamar yadda ya bayar da shaida, "a yayin da Najeriya ke fafutikar bunkasa karfin wutar lantarkin zuwa ma'aunin megawatts 10,000 cikin shekaru 18, kasar Masar tuni ta wuce wannan mataki cikin abin da bai wuce watanni 18 ba".
Dangote da ya kasance daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a doron kasa ya kuma shawarci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wata mafificiyar hanya ta yakar cin hanci da rashawa a kasar nan.
Kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito, Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin zaman karawa juna sani kan bunkasar tattalin arziki tare da masu ruwa da tsaki da aka gudanar cikin birnin Iko na jihar Legas.
Cikin shawarwari na yakar cin hanci da rashawa, Dangote ya nemi babban bankin Najeriya da kuma sauran bankunan kasar nan kan shigo da haja daga kasashen ketare domin samar da wani sabon tsari na bayar da bashi ga kananan 'yan kasuwa.
DAGA ISYAKU.COM
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN