PDP: Alhakin magudin da a ka yi wa Atiku ya jawowa Buhari rikici a mulki

Legit Hausa
Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta fito ta bayyana cewa kazamar fada da rikicin da a ke yi a fadar shugaban kasa da kuma cikin jam’iyyar APC bai rasa nasaba da zaben shugaban kasa.
A cewar, jam’iyyar adawar, magudin zaben da APC ta tafka a zaben 2019 ne ya dawo mata. Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP watau Mista Kola Ologbondiyan ne ya bayyana wannan.
“Mugun rikicin da a ke yi domin samun makaman gwamnati bayan murde zaben bana ya sake tona asirin APC da kuma wasu masu rike da madafan ikon kasar da ke cikin fadar shugaba Buhari.”
“Babu abin da ke gaban wadannan mutane na walwala da jin dadin mutanen Najeriya face samun mulkin kasar nan da kuma yi wa baitul-malin Najeriya rubdugu da rusa tattalin arziki.” Inji Ologbondiyan.
Kola Ologbondiyan ya fitar da wannan jawabi a Ranar 29 ga Watan Yuni, 2019 a madadin PDP ya na cewa:.
“A cikin ‘yan kwanakin nan, jama’a sun ga yadda abin takaici inda wasu na kusa da shugaban kasar su ka fito su ka tabbatarwa Duniya cewa wani daban ne ya ke juya akalar kasar nan.”
“Mutanen Najeriya sun ga yadda wasu ‘Ya ‘yan APC su ka fito su na zanga-zanga a Abuja a makon da ya wuce su na jero sunayen Abba Kyari, Mamman Daura da Isa Funtua a matsayin wadanda su ka hada ruwa gudu a mulkin Buhari.”
PDP ta cigaba da cewa:
“Daga baya an sake samun wata kishiyar zanga-zangar inda wadannan Miyagu su ka ce akwai hannun wani Gwamnan Arewa da kuma ‘Danuwansa da ya taba yin mulki a Kudu da hannu wajen wannan bore da a ke shiryawa don kurum cin ma burin 2023.”
PDP ta ce wannan abin kunya ya sake nuna yunwar manyan APC a tsirara da kuma kwadayin mulkinsu da tsabar son rai da tabbatarwa Duniya da cewa an murde zaben 2019 domin Buhari ya yi nasara.
Bugu da kari, Kola Ologbondiyan ya ce wannan ba komai ya nuna ba illa rashin kwarewar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda mulkinsa ya jawo tabarbarewar tattalin arziki da tsar
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN