Next Level: Zahra ta yi rubutu mai ratsa zuciya zuwa ga Buhari


Legit Hausa

Zahra Buhari, daya daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari ta yi amfani da kafar sada zumunta domin murnar fara mulkin mahaifinta karo na biyu. Ta yi rubutu mai ratsa zuciya ga mahaifinta a shafinta na Instagram.

A cikin rubutun, ta bayyana cewa Allah ne ya sake bawa mahaifinta ikon ya yiwa Najeriya jagoranci na adalci. Ta kuma yi addu'ar cewa abubuwa za su fi canja a wannan zangon na biyu. 

Ta yi fatan za a biya wa 'yan Najeriya bukatunsa sannan masu rike da mukamman gwamnati su mutunta 'yan Najeriya ta hanyar yi musu aiki tsakaninsu da Allah kuma 'yan Najeriya sune canjin da ake bukatar a kasar.Legit.ng ta ruwaito cewa 'yan Najeriya sunyi murnar rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki zango na biyu. 

'Yan kasar sun yi ta yada hotunnan shugaban kasar yayin taron rantsuwar kama aiki da akayi a dandalin Eagle Sqaure da ke birnin tarayya, Abuja.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN