Legit Hausa
Fittacen attajirin nan da ya yiwa duk wani bakar fata fintinkau da kuma zarra ta fuskar dukumar dukiya a fadin duniya, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana umul aba-isin da ya hana bunkasar tattalin arziki a Najeriya.
Fittacen attajirin nan da ya yiwa duk wani bakar fata fintinkau da kuma zarra ta fuskar dukumar dukiya a fadin duniya, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana umul aba-isin da ya hana bunkasar tattalin arziki a Najeriya.
Hamshakin
attajirin da ke kan sahu na gaba a nahiyyar Afirka ta fuskar tarin
arziki, ya ce kasar Najeriya ba za ta taba samun ci gaba ba ta hanyar
bunkasar tattalin arziki muddin aka dawwama cikin karanci da kuma rashi
na wutar lantarki.
Mamallakin
gidauniyar nan ta Dangote Foundation, ya ce a yayin da tattalin arziki
ya zamto tubalin ci gaba na kowace kasa a fadin duniya, Najeriya ba za
ta taba kai wa wannan munzali ba a sakamakon rashin wadatuwa da wutar
lantarki.
Kamar yadda ya bayar da shaida, "a
yayin da Najeriya ke fafutikar bunkasa karfin wutar lantarkin zuwa
ma'aunin megawatts 10,000 cikin shekaru 18, kasar Masar tuni ta wuce
wannan mataki cikin abin da bai wuce watanni 18 ba".
Dangote
da ya kasance daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a doron kasa ya kuma
shawarci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wata mafificiyar
hanya ta yakar cin hanci da rashawa a kasar nan.
Kamar
yadda jaridar PM News ta ruwaito, Dangote ya bayyana hakan ne a ranar
Asabar yayin zaman karawa juna sani kan bunkasar tattalin arziki tare da
masu ruwa da tsaki da aka gudanar cikin birnin Iko na jihar Legas.
Cikin
shawarwari na yakar cin hanci da rashawa, Dangote ya nemi babban bankin
Najeriya da kuma sauran bankunan kasar nan kan shigo da haja daga
kasashen ketare domin samar da wani sabon tsari na bayar da bashi ga
kananan 'yan kasuwa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI