• Labaran yau

  Muna nazari akan takardar da Ganduje ya aike mana – Shugaban ma’aikatan Sanus


  Legit Hausa

  Munir Sanusi, Shugaban ma’aikatan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yace masarautar na nazari akan irin abunda ke kunshe a takardar da aka aiko wa sarkin. Ofishin sakataren gwamnatin jihar ta aike da takardar neman ba'asi kan tuhumar da ake yi wa sarkin na yin bushasha da makudan kudaden masarauta a madadin Gwamna Abdullahi Ganduje. 

  Wata majiya ta ruwaito cewa ana zargin masarautar da yin fakaca da kudade. Shugaban ma’aikatan ya tabbatar da karban wasikar, cewa an bukaci sarki da ya bayar da amsa cikin sa’o’i 48. “Mun karbi takardar neman ba'asi a yau (Alhamis). 

  Gwamnatin ta nemi samun amsa cikin sa’o’i 48 daga mai martaba. Fada na nazari akan abunda takardar ya kunsa,” inji shi. A baya Legit.ng ta rahoto cewa tataburza dake tsakanin gwamnatin jahar Kano da fadar masarautar Kano ta kara zafafa, inda a yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da tsare tsaren tsige mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II daga kujerar sarauta.

  Majiyarmu ta ruwaito gwamnan ya aika ma Sarki wata takarda dake kunshe da dukkanin tuhume tuhumen da gwamnati ke masa dangane da almubazzarancin kudade, inda ya bukaci ya bashi amsa cikin sa’o’I 24.
   
  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Muna nazari akan takardar da Ganduje ya aike mana – Shugaban ma’aikatan Sanus Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });