Legit Hausa
Yayinda bikin ranar Demokradiyya ya kankama a farfajiyar
Eagle square dake babbar birnin tarayya Abuja, an nemi dukkan tsafin
shugabannnin kasar Najeriya an rasa a taron duk da an ajiye musu kujeru. Wannan
abu ya zo da mamaki kasancewar manyan al'umma kuma manyan abokan marigayi Cif
MKO Abiola wanda saboda gwagwarmayarsa aka canza ranar demokradiya zuwa ranar
12 ga Yuni.
Tsaffin shugabannin kasan sune, Janar Yakubu Gowon, Janar
Abdus salam Abubakar, Janar Ibrahim Babangida, Cif Olusegun Obasanjo, da Cif
Ernest Shonekan. Alkaluma sun bayyana cewa Obasanjo ya ki halartan taron ne
saboda kunya.
Ya kasance wanda ya ci gajiyar marigayi Abiola amma har ya
gama mulkinsa bai iya yin abinda shugaba Muhammadu Buhari yayi ba. Shi kuma Cif
Ernest Shonekan, an siffatashi matsayi daga daya cikin wadanda suka yaudari
Abiola da yan Najeriya saboda son mulki.
Hakazalika Janar Ibrahim Babangida, ba zai iya halarta ba
saboda shine ummul haba'isin soke zaben da Abiola ya samu nasara wanda hakan ya
kai ga rasa rayuwarsa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi