• Labaran yau

  Mazan da ke auren mata masu kiba sun fi farin ciki da jimawa a duniya - Masana  Legit Hausa

  Wani bincike da masana suka yi, ya bayyana cewa mazan da suke auren mata masu kiba sun fi farin ciki da kuzari, akan mazan da suke auren mata sirara. Binciken wanda wani kwararren masani mai suna Dr. Filemon Alvarado da kuma Dr. Edgardo Morales na Jami'ar kasar Mexico suka yi, ya bayyana cewa mata masu kiba basu da zurfin ciki, kuma basa boye-boye akan abubuwa na dangane da rayuwarsu, hakan ne ya sanya soyayya dasu take da dadi matuka.

  Binciken ya nuna cewa, matan masu kiba suna sanya mazajen su farin ciki sau 10 fiye da wadanda suke auren sirara. Na biyu shine, mata masu kiba suna da wata ni'ima wadda sai wanda ya aura zai gane. 

  Na uku kuma binciken ya nuna cewa, mata masu kiba suna murmushi tare da kwantarwa da mazajen su hankali fiye da da sirara, sannan kuma sun fi siraran mata taimakawa wajen neman mafita idan an shiga matsala. Na karshe shine, mata masu kiba ana samun su wurin taimakawa mazajensu akan duk wata bukata tasu, hakan yasa zama dasu yake da dadi matuka.

  Binciken ya gano cewa mata sirara, suna da zurfin ciki, kuma basu da dadin zama sannan basu iya soyayya ba, hakan yasa zama dasu yake zama tashin hankali. A karshen binciken, masu binciken sun bayyana cewa mazajen da suka auri mata masu kiba sun fi jimawa a duniya, kuma sunfi yin rayuwa cikin farin ciki.


  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mazan da ke auren mata masu kiba sun fi farin ciki da jimawa a duniya - Masana Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });