Matasa a Taraba sun far ma ofishin yan sanda, sun saki makeran bindiga 3 sannan suka yi wa yan sanda dukan tsiya

Legit Hausa

Wasu matasa a garin Wukari, jihar Taraba sun far ma ofishin yan sanda a yankin sannan suka kubutar da wasu mutane uku da yan sanda suka kama kan laifin kera bindigogi.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jami’an yan sandan sun kama mutane ukun ne a garin Wukari a ranar Lahadi bisa zargin kera bindigogi daga Jalingo sannan suka kai su ofishin yan sanda don tsaro.
An tattaro cewa jami’an tsaron na shirye-shiryen tafiya da masu laifin Jalingo ne a lokacin da matasan suka far ma ofishin yan sandan sannan kuma suka kubutar da masu laifin.
Wani majiyi wanda ya ki bayyana sunan shi ga Daily Trust a ganawar wayar talho ya bayyana cewa matasan sun kai hari ofishin yan sanda, inda suka yiwa yan sandan duka sannan suka kubutar da masu laifin.
Har ila yau idan zaku tuna a 2013 ne matasan garin suka kona ofishin yan sanda da ke garin sanadiyyan rikicin addini.
A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP David Misal yace ba a kai rahoton lamarin ga rundunar ba amman yayi alkawarin tuntuban ofishin hukumar na reshen Wukari don bincike.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN