Matakin Nasara: Jamiyyu 10 sunyi Mubaya'a ga Matawalle


Legit hausa

Jam'iyyun siyasa guda 10 a jihar Zamfara sun ce babu hannunsu a kalubalantar da ake yima Matawalle a kotu na nasararsa zama gwamnan jihar wanda jam'iyyar APP ta ce ta shigar. Kamfanin dillacin labaai na Najeriya ya ruwaito cewa dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APP, Alhaji Zayyanu Haske, ya shigar da kara a kotun zabe dake Abuja.

Haske na rokon kotun da ta soke zaben da ya kawo Matawalle a matsayin gwamnan jihar. Dan takarar na jam'iyyar APP na ikirarin cewa da goyan bayan wasu jam'iyyu a jihar ya shigar da karar. A lokacin da suke mayar da martani, shuwagabannnin jam'iyyu guda 10, karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), Alhaji Musa Mai-mai, sunce babu ruwansu a cikin karar kuma ba wanda yayi shawara dasu a lokacin da ya aka shigar da karar.

"Ba ayi shawara da mu ba, mun yarda da hukuncin da kotun koli ta Najeriya tayi, wanda ta soke zaben fidda gwani na jam'iyyar APC wanda sanadiyyar hakan ne Matawalle ya zama gwamna." A lokacin da yake ganawa da yan Jarida a Gusau, Shugaban jam'iyyar ta AD Alhaji musa, ya ce wadanda ke kalubalantar Matawalle na "yin adawa marar kan gado wanda hakan ba dai dai bane." "Mu babu ruwanmu a tafiyarsu, muna so duniya ta sani cewa su kadai ke tafiyarsu" Ya kara da cewa "Mafi yawan shuwagabanni da dattawan jihar nan sunyi mubaya'a ga sabuwar gwamnatin ciki ko hadda tsohon gwamna Abdul Aziz Yari.

A sabida haka muna tunanin zasu bi wannan gwamnati za kuma su taimaka mata wajen ganin ta cimma nasara." Shugaban na jam'iyyar AD yayi kira ga al'ummar jihar da su yi biyayya ga gwamnatin su kuma taya ta da addu'a don ganin cewa tayi nasara musamman wajen magance matsalolin tsaro. Sauran jam'iyyun da suka janye hannunsu daga tuhumar da ake ma Matawalle sun hada da PRP, SDP, ID, HD, ASD, MMN, NAC, KOWA da kuma FRESH.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN