Masu garkuwa da mutane sun nuna mun kabarin yarana bayan sun karbi N2.5m kudin fansa – Inji wani Alhaji


Legit Hausa

Yan bindigan da suka yi garkuwa da yara biyu a watan da ya gabata a kauyen Dan-Ali da ke jihar Katsina a jiya Alhamis, sun fada ma iyayensu cewa an kashe yaran a lokacin da rundunan sojin sama ta kai hari. Mahaifinsu yace maimakon a sako su bayan sun karbi kudin fansa naira N2.5 million, yan bindigan sun jagorance shi zuwa kabarurrukan yaransa.

Anyi garkuwa da Anas Idris da Ibrahim Idris da misalin karfe 1:30 na tsakar dare a ranar 27 ga watan Mayu a lokacin da suka kai hari gidan. Yan bindigan sun bukaci naira miliyan Miliyan 20 a matsayin kudin fansa wanda daga baya an bada naira miliyan 2.5.Mahaifinsu, Alhaji Idris Garba Dan Ali, a wani hiran shi da manema labarai yace:

“Naje domin na hadu dasu (Yan bindigan) a kauyen Leletu na karamar Hukumar Dan Musa. Suka ce in jira su na dan lokaci. Bayan dan lokaci kadan, su shida suka zo sannan bayan sun karbi kudin, suka bukaci in fada musu wanda nazo ceto.

“Sai suka fada mani cewa yan kwanaki da suka gabata rundunar sojin sama sun gudanar da aikin tayar da yankin kuma cewa an kashe yarana a harin. Sai suka nemi na bisu domin ganin kabarinsu, amma naki sannan na fada masu cewa tunda an kashe su, na bar komai a hannun Allah kuma Allah ya ji kansu da rahma.”

Wani Jami’in sojin sama wanda yayi magana bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba ya karyata zargin da yan fashin suka yi, na cewa rundunan ce ta kashe yaran a harin da suka kai ma yan fashin a jejin.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN