Masu bincike na kasar Ingila sun antayo Najeriya akan batun Diezani

Legit Hausa
A shirye shiryen da ake yi dangane da fara shari’ar tsohuwar minstan albarkatun man fetur, Diezani Alison Madueke, masu bincike na kasar Ingila sun hallara a Najeriya don yin bincike na karshe game da batun.
Masu binciken sun gana da jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) don kara samun bayanai, kuma yanzu haka sun kai sati guda a Najeriya.
Babu tabbacin cewa binciken zai dauki fiye da sati daya, amma akwai alamu masu binciken sun samu kwararan shaidun kuma sun baukaci karin bayani akan wasu shaidun da suke a hannunsu.
Legit Hausa
An gano cewa dokar da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ma hannu satin da ya gabata ta taimakekeniya tsakanin kasashe akan batutuwan laifuffuka, za ta taimaka kwarai wajen kwace kadarorin Diezani a nan gida Najeriya da kuma kasashen waje.
A yanzu dai, hukumar EFCC ta gano wasu kudade da Diezani ta wawura da yawansu ya kai Naira biliyan 47.2 da miliyan 487.5 na dalar Amurika. Hukumar ta kuma yi ikirarin cewa Diezani na da Naira 23,446,300,000 da kuma miliyan biyar na dalar Amurika (kimanin Naira biliyan 1.5) a asusun ajiya na bankuna daban daban a Najeriya.
Hukumar ta EFCC ta kuma samu izinin kotu da ta kwace wasu kadarorin Diezani da suka hada da wani gini dake a Banana Island da kudinshi ya kai miliyan 37.5 na dalar Amurika, da dai sauransu.
Masu binciken na kasar Ingila dai sun zo Najeriya ne don su ida tattara bayanai akan binciken da sukeyi wanda aka fara tsawon shekaru hudu da suka wuce. An kama tsohuwar ministan tun ranar 2 ga watan Oktoba 2015, kuma an tsare ta ne akasar Ingila.
Duk da dai babu tabbaci ko za a maido Diezani Najeriya, alamu sun tabbatar da cewa sakamakon hujjojin da aka samu kwarara za a iya yi mata shari’a ko a Najeriya ko kuma a can Ingila.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN