Masaraauta ba wasa bace: An gargadi Gwamnatin Kano da ta yi taka tsan-tsan

Legit Hausa A daren Lahadin da ta gabata ne tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, ya gargadi gwamnatin jihar Ka...


Legit Hausa

A daren Lahadin da ta gabata ne tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, ya gargadi gwamnatin jihar Kano da ta tabbatar da yin taka tsan-tsan yayin gudanar da binciken a kan Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammad Sanusi II. 

Tsohon sakataren gwamnatin kasa ya nemi gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da ta tabbatar ba ta sabawa ka'ida ta shari'a ba a yayin takaddamar Masaurautar Kano da wargi ba ya kusantar ta. 

Yayale wanda ya kasance tsohon shugaban ma'aikata gwamnatin Tarayya kuma tsohon Ministan Tsaro, ya ce duk da goyon bayan jam'iyyar adawa ta PDP, gwamnatin jihar Kano ta tuna cewa Sarki Sanusi ya kasance uba ga dukkanin al'ummar jihar. 

Yayin ganawar sa da manema labarai ta hanyar wayar tarho, tsohon Ministan ya kuma tunatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje cewa ya kasance jagora ga dukkanin al'ummar jihar Kano duk da sabani na ra'ayin siyasa. 

Yawale wanda shi ne mai rike da rawanin Ajiyan Katagum, ya gargadi gwamnatin Kano kan cewa muddin ta ci gaba gudanar da al'amura tare da mu'amalantar masarautar Kano kamar yadda ta ke yi a yanzu, babu shakka ba za a kwashe lafiya ba cikin ilahirin Arewacin Najeriya baki daya. 

Ana iya tuna cewa gwamnatin Kano na zargin fadar Mai Martaba Sarki Sanusi da almundahar kimanin Naira biliyan 3.4 na masaurautar Kano. Sai dai yayin mayar da martani fadar ta ce abin da ta riska yayin cin gajiyar mulki bai wuce Naira biliyan 1.8 ba. 

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kafa kwamitin wasu gwamnoni hudu na jihohin Ekiti, Kebbi, Jigawa da kuma na Neja akan shiga tsakani tare da tabbatar da sulhu tsakanin gwamna Ganduje da kuma Sarki Sanusi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi 
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,110,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2981,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,354,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Masaraauta ba wasa bace: An gargadi Gwamnatin Kano da ta yi taka tsan-tsan
Masaraauta ba wasa bace: An gargadi Gwamnatin Kano da ta yi taka tsan-tsan
https://1.bp.blogspot.com/-TWGgwGLtIlE/XP5v03tWXII/AAAAAAAAWNc/MMIMmO2xi2YyVAw5VIhxhM9KT63pt9wmgCLcBGAs/s1600/sanusi-ganduje.jpg
https://1.bp.blogspot.com/-TWGgwGLtIlE/XP5v03tWXII/AAAAAAAAWNc/MMIMmO2xi2YyVAw5VIhxhM9KT63pt9wmgCLcBGAs/s72-c/sanusi-ganduje.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/06/masaraauta-ba-wasa-bace-gargadi.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/06/masaraauta-ba-wasa-bace-gargadi.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy