Manyan ma’aikatan
gwamnati karkashin kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati (ASCSN) ta ce za
ta shiga yajin aiki sakamakon karya dokar ma’aikatan gwamnati da
yarjejeniyar da suka kulla da hukumar inshora ta Najeriya (NAICOM).
ASCSN ta ce sharuddan yarjejeniyar da aka rattafa ma hannu a ministirin
kwadago a cikin watan Agusta na 2018, sun hada da samar da kudin alawus
na man fetur da dizil, da kuma ba sauran ofisoshi mahimmanci.
Kungiyar ta ce zata shiga yajin aikin idan hukumar ba ta zartar da
sharuddan yarjejeniyar ba nan da kwana bakwai.
A jawabin da sakataren kungiyar, Isaac Ojemheken, ya sanyawa hannu,
ASCSN, ta ce “Muna a matse shi ya sanya muke sanar maku cewa mambobin
kungiyar ASCSN ta yi taro a Abuja a ranar 24 ga watan Yuni 2019, kuma an
cimma matsaya cewa a ba hukumar inshora wa’adin kwana bakwai don ta
tabbatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar mu.”
“Ya zama dole mu sanar cewa ASCSN ba ta da laifi idan har aka shiga
yajin aiki sakamakon rashin biya ma yan kungiyar bukatunsu cikin kwana
bakwai.”
“Haka zalika, ya zama dole mu sanar cewa babban sakataren ministirin
kwadago da aiki, babban sakataren ministirin kudi, babban daraktan yan
sandan cikin gida (DSS), babban sifeton yan sanda, da shugaban hukumar
inshora duk sun sanya hannu a wannan takarda."
“Muna cikin rashin jin dadi muke bayyana maku cewa bayan shekara biyu da
cimma yarjejeniyar farko a ranar 26 ga watan Satumba 2017, hukumar ta
inshora ta ki tabbatar da yarjejeniyar da gan gan duk da rokon da aka yi
masu." Read more: https://hausa.legit.ng/1245706-yajin-aiki-maaikatan-gwamnatin-tarayya-sun-ba-da-waadin-kwana-7.html
Legit Hausa
Manyan ma’aikatan gwamnati karkashin kungiyar manyan
ma’aikatan gwamnati (ASCSN) ta ce za ta shiga yajin aiki sakamakon karya dokar
ma’aikatan gwamnati da yarjejeniyar da suka kulla da hukumar inshora ta
Najeriya (NAICOM). ASCSN ta ce sharuddan yarjejeniyar da aka rattafa ma hannu a
ministirin kwadago a cikin watan Agusta na 2018, sun hada da samar da kudin
alawus na man fetur da dizil, da kuma ba sauran ofisoshi mahimmanci.
Kungiyar ta ce zata shiga yajin aikin idan hukumar ba ta
zartar da sharuddan yarjejeniyar ba nan da kwana bakwai. A jawabin da sakataren
kungiyar, Isaac Ojemheken, ya sanyawa hannu, ASCSN, ta ce “Muna a matse shi ya
sanya muke sanar maku cewa mambobin kungiyar ASCSN ta yi taro a Abuja a ranar
24 ga watan Yuni 2019, kuma an cimma matsaya cewa a ba hukumar inshora wa’adin
kwana bakwai don ta tabbatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar mu.”
“Ya zama dole mu sanar cewa ASCSN ba ta da laifi idan har
aka shiga yajin aiki sakamakon rashin biya ma yan kungiyar bukatunsu cikin
kwana bakwai.” “Haka zalika, ya zama dole mu sanar cewa babban sakataren
ministirin kwadago da aiki, babban sakataren ministirin kudi, babban daraktan
yan sandan cikin gida (DSS), babban sifeton yan sanda, da shugaban hukumar
inshora duk sun sanya hannu a wannan takarda."
“Muna cikin rashin
jin dadi muke bayyana maku cewa bayan shekara biyu da cimma yarjejeniyar farko
a ranar 26 ga watan Satumba 2017, hukumar ta inshora ta ki tabbatar da
yarjejeniyar da gan gan duk da rokon da aka yi masu."
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
TSARO