Malam dogo ya isa garin Ibadan a jihar Oyo

Legit Hausa Ana cike da murna a garin Ibadan sakamakon isowar jirgin kasa garin Ologuneru a Ibadan babban birnin jihar Oyo mai tsa...


Legit Hausa

Ana cike da murna a garin Ibadan sakamakon isowar jirgin kasa garin Ologuneru a Ibadan babban birnin jihar Oyo mai tsawon kilomita 152. Shugaban hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya Alhaji Ibrahim Hassan yace za a ida sauran kilomita biyar din da ta rage daga nan zuwa karshen wannan watan na Yuni.

Alhassan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da yan kwangila da sauran masu ruwa da tsaki a farfajiyar aikin jirgin kasan a garin Ologuneru bayan da ya duba aikin tun daga garin Iju na jihar Legas. Ya ce za a sanya layin jirgin kasa guda biyu na zauwa da na dawo wa mai kimanin tsawon kilomita 133 daga nan zuwa watan Yuli na wannan shekarar.

Ya kara da cewa bayan an gama sanya layukan ne za a dukufa wajen ganin an samar da sauran abubuwa kamar su tashar jirgin kasan. Ya ce za a gama gina kananan tashoshin jirgin kasan tsakanin Legas zuwa Ibadan kuma za a gama ginin daga nan zuwa karshen wanna shekarar domin fara sufurin matafiya Ya ce "Ana aiki a dukkanin tashoshin jirgin kasa. Idan kana da aiki irin wannan dole sai ka fi ba wani mahimmanci, mu kuma mun zabi aikin gina titin jirgin kasan.

" "Da zarar an gama aikin wanda muna da tabbacin za a gama kafin karshen watan Yuli, to zamu maida hankali wajen gina sauran wuraren aiki na jirgin kasan". Alhassan ya yabawa shugaban kasa wajen kokarin sa na samar da ingantattun jiragen kasa a fadin kasannan.

Ya kuma jin jina ma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya jajirce wajen ganin an samu canji ta fannin sufurin jirgin kasa. Ya bayyana cewa dalilin da yasa aka samu tsaiko a aikin da ke gudana a Legas, na da alaka da wasu matsaloli da suke fuskanta. Ya bayyana cewa matsalolin sun hada da gine ginen da akayi ba a bisa ka'ida ba, bututun man fetur da na ruwa da kuma wayoyin wutar lantarki da ke kan hanyar.

Shugaban hukumar ya bada albishir din cewa daga nan zuwa karshen wannan watan za a samu karin kawunan jirgin kasa guda biyu don a hada da wayanda ke kasa don fara suifurin matafiya. Yace za a fara sufurin cikin watan Agusta kuma hukumar ta tanaji wuraren da zata rika siyar da tikitin jirgin.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,110,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2981,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,354,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Malam dogo ya isa garin Ibadan a jihar Oyo
Malam dogo ya isa garin Ibadan a jihar Oyo
https://1.bp.blogspot.com/-ajGzZbgzqs4/XQOKJZqCZJI/AAAAAAAAWRs/Eh5t9a-VhXYMZJU9ntCSRx-nfT7qS1QCQCLcBGAs/s400/train1.jpg
https://1.bp.blogspot.com/-ajGzZbgzqs4/XQOKJZqCZJI/AAAAAAAAWRs/Eh5t9a-VhXYMZJU9ntCSRx-nfT7qS1QCQCLcBGAs/s72-c/train1.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/06/malam-dogo-ya-isa-garin-ibadan-jihar-oyo.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/06/malam-dogo-ya-isa-garin-ibadan-jihar-oyo.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy