Majalisar zartarwa: Buhari zai tuntubi shugabannin APC na kasa da jiha

Legit Hausa

Ga dukkan alamu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar tuntubar shugabannin jam'iyya mai mulki a fadin jihohi 36 a kokarinsa na kafa majalisarsa na gaba, jaridar The Nation ta ruwaito.
Majiyoyi sun kawo cewa Shugaban kasar ya shirya aiki tare da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matakin kasa da jiha, a kokarinsa na tafiya tare da kowa.
Wata majaliyar jam’iyyar tace: “Shugabancin jam’iyyar na sanya ran ji daga Shugaban kasa nan ba da jimawa ba kan gudunmawarta wajen tsarin zabar majalisar. Kuma an bukaci dukkanin rukunin shugabannin jam’iyyar su kasance cikin lamarin.”
Wani Shugaban jam’iyya mai mulki na jiha ma ya tabbatar da hakan ga majiyarmu cewa ana sanya ran jam’iyyar za ta taka gagarumin rawar gani wajen kafa majalisar Buhari na gaba.
“Shugaban kasar yace zai yi aiki tare da jam’iyyar kuma mun yarda dashi,” inji majiyar.
Ya kara da cewa: "An sanar dani da abokan aikina da muyi hakuri mu saurari bayanai kan wadanda za su wakilci jihohinmu a majalisar zartarwa na tarayya."
An kuma tattaro cewa da dama daga cikin tsoffin ministocin Shugaban kasar na ta kamun kafa a wajen jami’ai da shugabannin jam’iyyar domin a sake zabarsu a majalisar.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN