Majalisar dokoki ta tara: PDP na son Dogara ya zama Shugaban marasa rinjaye

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci mambobin jam’iyyar a majalisar wakilai, da su zabi shugabanninsu sannan su sanar da jam’iyyar hukuncinsu a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni.
A cewar jaridar ThisDay, wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa an bukaci yan majalisar wakilan da su zabi shugabanninsu bayan sun duba da kytau, kamar yadda aka yi a majalisar fdattawa, a lokacin da suka gana tare da shugabancin jam’iyyar a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuni.
Legit.ng ta tattaro cewa ana so tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon Yakubu Dogara ya haye matsayin Shugaban marasa rinjaye.
Majiyar ta rahoto cewa: “A halin da ake ciki, a matsayinsa na tsohon kakakin majalisar wakilai, ya fara jagoranci kuma shine ke ta jagorantar mambobinmu a majalisar wakilai.”
Majiyar ta kara da cewa: “Zai samu kujerar, sai dai idan yaki amincewa.”
Wata majiya ta bayyana cewa Shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus ya jagorancin ganawar. An tattaro cewa an zabi Dogara a matsayin Shugaban marasa rinjaye domin guje ma zargin tursasa wani jagora kan mambobin.
An kuma tattaro cewa Hon Ndudi Elumelu da Dr Ossai Ossai, yan majalisar wakilai biyu daga Delta, na zawarcin matsayin Shugaban marasa rinjaye.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN