Legit Hausa
Tsohon shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa, Sanata Ali
Ndume, a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ya bayyana cewa dole majalisar dattawa
na tara tayi aiki don kare yancin ta don gujewa rigingimu a zaman majalisar.
Sanatan mai wakiltan Borno ta kudu ya bayyana cewa abu guda da ya kamata kowace
majalisa ta kasance da shi ita ce yanci wacce zata yi iya kokarinta wajen kare
wannan yancin.
Ndume wanda ya kasance daya daga yan takara dake kan gaba a
wajen neman shugabancin majalisar dattawa yayi magana yayinda yake bada
gudumuwar shi a taron bankwana na majalisar dattawa ta takwas. Ya bayyana cewa
banbancin dake tsakanin damukardiyya da kuma gwamnatin soja shine yancin
majalisar dokoki.
Ya dage cewa dole a girmama majalisar a matsayin alamar
damukardiyya wacce dole a kare yancinta a dukkan lokuta. Ya bayyana cewa
majalissan ta kasance ginshikin damukardiyya a kowace kasa. A baya Legit.ng ta
rahoto cewa Sanata Ali Ndume, ya ce ba zai janye takarar sa ba yayin babban
zaben da za a gudanar a ranar 11 ga watan Yuni a zauren majalisar dake garin
Abuja.
Ndume wanda ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema
labarai a ranar Alhamis, ya ce ba ya bukatar kai wa shugaban kasa Muhammadu
Buhari wata ziyara domin sauya ra'ayin sa na janye takarar neman shugabancin
sabuwar majalisar dattawan kasar nan.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Sanata Ndume ya ce
ba ya da wata bukatar neman shawarar shugaban kasa Buhari domin yanye takara ga
Sanata Ahmed Lawan wanda ya kasance daya daga cikin masu hankoron kujerar
jagoranci a majalisar dattawa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi