Legit Hausa
Jastis Inyang Ekwo, alkalin wata babbar kotun gwamnatin
tarayya, ya amince da aika wa dan takarar neman shugabancin majalisar wakilai,
Femi Gbajabiamila, takardar sammaci ta hannun lauyansa, Olasupo Azeez.
An shigar da karar neman haramta wa Gbajabiamila zama mamba
a majalisar wakilai a gaban kotun bisa dogaro da wani laifi mai nasaba da zamba
da ya taba aikata wa lokacin da yake aikin lauya a kasar Amurka.
Jastis Ekwo ya ce aika sammaci ta hannun lauyan ya zama
tilas ne saboda kotun ta gaza mika sammacin zuwa ga Gbajabiamila hannu da
hannu. "Irin wannan kara na jan hankalin jama'a, a saboda haka dole ka
kasance cikin shiri," alkalin ya fada wa Azeez. Sakamakon haka, Jastis
Ekwo ya daga sauraron zuwa ranar Juma'a, 7 ga watan Yuni.
Wani mutum mai suna Philiph Undie ne ya shigar da karar
Gbajabiamila ta hannun lauyansa, Barista Ayodele Justice. Ya shaida wa kotun
cewar Gbajabiamila bai cancanci zama mamba a majalisar wakilai ba saboda an
taba gurfanar da shi a wata kotun kasar Amurka da laifin zambar kudi $25,000.
A cewar Undie, kasar Amurka ta kwace lasisin aikin lauya na
Gbajabiamila tare da dakatar da shi tsawon watanni 36 shekara uku).
Andie ya ce
Gbajabiamila, lokacin yana amfani da sunan Femi Gbaja, ya taba karbar kudin
diyyar da aka biya wani mutum da ya kare a kotu amma maimakon ya bawa mutumin
kudinsa sai ya zuba su a asusun bankinsa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi