Lai Mohammed ya ki bayyana a gaban kotu game da batun kudi N2.5bn


Legit Hausa

Lai Mohammed, tsohon minstan labarai, a ranar Laraba, ya ki bayyana a gaban Mai shari’ah Folashade Ogunbanjo Giwa na babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja, don yayi bayani akan kudi Naira biliyan 2.5 da aka baiwa kamfanin Pinnacle Communication.

A zaman na ranar Laraba, an cigaba da sauraren karar da ake yima babban darakta na watsa labarai, Ishaq Kawu Modibbo, da kamfanin Pinnacle Communication da wasu mutum biyu. Tsohon ministan na labarai, na cikin sunayen da mai gabatar da kara, Henry Emore ya bayar a matsayin shaidun hukumar hana ta'annaci da kudin kasa (ICPC) kuma ana tsammani zai bayyana gaban kotu don ya bayar da shaida a matsayinsa na tsohon minista da ya bayar da umurnin a biya 2.5 ga kamfanin Pinnacle.

Amma, bayan da ya kira shaidu biyu, mai gabatar da karan ya gaya ma kotu cewa ya so ya kira shaidarshi na gaba, tsohon ministan labarai amma bai samu halartar zaman kotun ba. Emore ya bayyana ma kotun cewa Lai Mohammed yayi tafiya zuwa kasar waje amma ana tsammanin zai dawo Najeriya kafin ranar 31 ga watan Yuli.

Haka zalika ya bayyana ma kotu cewa Lai Mohammed ya bayar da shaidarshi a rubuce ga ICPC, a matsayinshi na tsohon minista. Mai gabatar da karar ya kuma bayyana ma kotu cewa sauran shaidun da ya so ya kira sunyi tafiya zuwa kasar Saudiyya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN