Kuma dai: An kara samun wata mata da ta caka wa mijinta wuka har ya mutu

Legit Hausa

Wata mace mai shekaru 20, Makoduchukwu Ndubisi a ranar Asabar ta caka wa mijinta wuka har lahira a ugarin Nsugbe da ke karamar hukumar Anambra Ta Gabas na jihar Anambra.
Ndubisi ta caka wa mamacin, John Bosko Ngu wuka a kirjinsa ne sakamakon rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu da har yanzu ba a tabbatar ko mene ba.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an kai gawar mamacin dakin ajiye gawarwaki na asibiti.
Ya kara da cewa an fara gudanar da bincike domin gano musababbin afkuwar kisar.
Ya ce, "misalin karfe 8 na safiyar yau, 'yan sandan da ke aiki da caji ofis mai lamba 33 sun kama wata Makoduchukwu Ndubisi mai shekaru 20 mai zaune a gida mai lamba 16 Donking Street a garin Nsugbe da ke karamar hukumar Anambra Ta Gabas a jihar Anambra.
"Wanda ake zargin da samu rashin jituwa da mijinta, wani John Bosko Ngu dan shekaru 35 da ke zaune a 16 Donking Street kuma ta caka masa wuka a kirji.
"Yan sanda sun garzaya wurin da abin ya faru inda su kayi gaggawar kai wanda aka caka wa wukar asibitin Boromoeo a Onitsha amma da isarsu likitoci suka tabbatar ya mutu.
"An ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki na asibitin an kuma gano makamin da akayi kisar da shi sannan an fara bincike domin gano abinda ya yi sanadin afkuwar kisar."
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN