Legit Hausa
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo jiya Alhamis, 27 ga
watan Yuni, ya bukaci matasa da su nemi takarar mukaman shugabanci a kasar.
Yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar matasan Najeriya a gidansa da ke
harabar dakin karatunsa a Abeokuta, Obasanjo ya ce: “kada ku bari kowa ya fada
muku cewa kun yi kankanta da neman shugabanci, na soma bada gudumuwana a duniya
a lokacin da nake aiki a kasar Congo a shekarar 1960, a lokacin ina dan shekaru
24.
"A lokacin da na tafi filin daga na kasance dan kasa da
shekara 35, a lokacin ne na zama shugaban kasa a mulkin soja, ban kai shekaru
40 ba a lokacin." Obasanjo ya nuna damuwa cewa sama da yara miliyan 13 ne
basa zuwa makaranta a Najeriya. Yace: “duk abin da nayi, nayi ne saboda na
kasance mai ilimi kuma mai kishin kasar Najeriya.
“Da banyi karatu ba da ban kai matsayin yin abubuwan da nayi
ba, a yau ina matukar bakin cikin cewa fiye da yaran Najeriya miliyan 13
wadanda ya kamata suna a makaranta sun bar makaranta.”
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
SIYASA