Legit Hausa
Kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta yi watsi da
bukatar hukumar zabe ta kasa (INEC) da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na
neman kotun ta kori karar da jam'iyyar PDM ta shigar a gaban ta. Buhari da
INEC, kasancewarsu cikin wadanda jam'iyyar ke kara, sun bukaci kotun ta kori
karar ne bisa dogaro da cewa ba ta shigar korafin ta a gaban kotun bisa ka'ida
ba, kamar yadda doka ta tanada.
Babban alkalin kotun,
Jastis Mohammed Garba, ya ce jam'iyyar PDM ba ta saba wata ka'ida ba a karar da
ta shigar. Ya ce PDM ta gabatar da dukkan wasu korafe-korafe tare da kalkale
komai a ranar 15 ga watan Afrilu, wanda ya kasance cikin wa'adin da aka tsayar
na kammala gabatar da korafi kafin ranar 21 ga watan Afrilu.
Jastis Garba ya kara da cewa jam'iyyar PDM ta bi tsarukan da
dokokin zabe suka tanada, a saboda haka INEC da shugaba Buhari basu fahimci
yadda lamarin ya ke ba.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
SIYASA