Legit Hausa
A ranar Litinin wata kotun ma'aikata dake zamnata a Abuja ta
bawa rundunar sojin Najeriya umarnin mayar da manjo janara Nwokoro Ijioma bakin
aikinsa. Mista Ijioma na daga cikin manyan jami'an soji 38 da rundunar soji ta
yiwa ritayar dole a shekarar 206.
Da take yanke hukunci, alkaliyar kotun, Edith Agbakoba, ta
ce akwai shaidar cewar ba a bi ka'ida ba wajen tilasta Ijioma yin murabus. Ta
ce ba a sanar da Ijioma laifinsa ko gurfanar da shi a gaban kotun sojoji bisa
kowacce tuhuma ba kafin a yi masa ritayar dole.
Kazalika ta bayyana cewar ba a bawa Ijioma damar ya kare
kansa ko gabatar da wani uzuri ba kafin a sallame shi daga bakin aiki. Bisa
dogara da wadannan hujjoji ne ta sanar da cewar ritayar da aka yi wa Ijioma
haramtacciya ce da ta saba wa ka'ida, a saboda haka ba ta da wani tasiri.
Ta bayyana cewar har yanzu Ijioma jami'i ne a rundunar sojin
Najeriya. Alkaliyar ta jingine takaradar ritayar da aka yi wa Ijioma mai dauke
da kwanan watan 9 ga watan Yuni na shekarar 2016. Alkaliyar ta bayar da umarnin
mayar da Ijioma kan mukamin da yake kai kafin a sallame shi tare da biyansa
dukkan hakkokinsa na tsawon lokacin da aka sallame shi.
Sannan ta haramtawa hukumar soji da dukkan wadanda aka
Ijioma ya shigar da su kara daukan wani mataki da zai shafi ko da dakatar da
hakkokin Ijioma ko kuma muzguna masa. Ta kuma umarci rundunar soji ta biya shi
N200,000 a matsayin kudin da ya kashe wajen shigar da kara a gaban kotun.
Ijioma ya garzaya gaban kotun ne yana neman ta jingine ritayar dolen da
rundunar soji ta yi masa a kan korafin cewar ba a bi ka'ida ba wajen yin hakan.
A cikin wadanda Ijioma ya ambata a cikin takardar shigar da
kara a gaban kotun akwai shugaban rundunar soji, babban hafsan rundunar sojoji
da kuma ministan tsaro. Read more:
https://hausa.legit.ng/1241689-kotu-ta-umarci-rundunar-soji-ta-mayar-da-wani-janar-da-ta-kora-daga-aiki.html
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI