Kotu ta sake amshe kujerar majalisar wakilai daga hannun APC ta mika ma PDP


Legit Hausa

Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, ta soke nasarar da zababben sabon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zaki ta jahar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC, Omar Tata ya samu. Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Bello Kawu ne ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu, inda ya bayyana sanar da sunan Tata a matsayin wanda ya lashe zaben a matsayin haramun.

Don haka Alkalin Bello Kawo ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC data mika ma abokin hamayyarsa na PDP Jatau Muhammad Auwal shaidar samun nasarar lashe zabe, wanda shine yazo na biyu a zaben. 

A cewar kotun, jam’iyyar APC bata dan takara, kuma babu yadda za’ayi ta tsayar da dan takara a zaben kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Zaki ta jahar Bauchi a zaben 2019. Dalili kuwa shine, dan takarar jam’iyyar PDP, Jatau Muhammad Auwal ya shaida ma kotun cewa dan takarar jam’iyyar APC bai cancanci tsayawa takara ba sakamakon jam’iyyar bata gudanar da zaben fidda gwani ba wajen tsayar dashi takara ba. 

Don haka Jatau ya kalubalanci nasarar da hukumar INEC tace Tata ya samu a zaben watan Feburairu na 2019, ita kotun ta gamsu da jawaban Jatau, inda ta bayyana kuri’un da Tata ya samu a matsayin haramtattu, don haka ta sokesu duka, da haka Jatau ya zamo sabon dan majalisa. 

Wannan hukunci ba shi bane farau ba da kotu take kwace ma jam’iyyar APC mukamanta tana mikasu ga jam’iyyn hamayya, musamman ma jam’iyyar PDP, kuma hakan ya faru ne sakamakon karan tsaye da jam’iyyar APC tayi ma dokokinta da dokokin zabe a wasu jahohin da take da mulki.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN