• Labaran yau

  Kotu ta bayar da umarnin tsare wani limami da aka samu da laifin lalata da yarinya a Masallaci


  Legit Hausa

  A ranar Litinin ne wata kotun sauararon kararrakin da suka shafi fyade da rigingimun cikin gida da ke Ikeja a jihar Legas ta bayar da umarnin tsare wani malamin Islama, Abdulsalam Salaudeen, bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa zarginsa da aikata fyade ga wata karamar yarinya mai shekaru biyar a cikin Masallaci. Alkalin kotun, Jastis Abiola Soladoye, ya amince da bukatar mai gabatar da kara na neman a tsare mai laifin. Bayan ya amsa bukatar mai gabatar da karar, Soladoye ya daga fara sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

  Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar ana tuhumar Salaudeen, mai shekaru 43, da laifin aikata fyade ga wata karamar yarinyar da ke karkashin kulawarsa. Mai gabatar da kara, T. Olanrewaju-Dawodu, ta shaida wa kotu cewa Salaudeen ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2018 a harabar Masallacin Olorunbabe da ke lamba 15 a titin zuwa fadar unguwar Igando da ke daura da Legas.

  Olanrewaju-Dawodu, ta ce an kama Salaudeen, wanda aka fi kira da Alfa (Liman da harshen Yoruba), ta hanyar amfani da na'urorin daukar hoton bidiyo da wasu mutane da ke zarginsa suka dasa a harabar Masallacin. Sai dai, Salaudeen, mazaunin gida mai lamba 16 a kan titin Awoyemi da ke unguwar Ikotun, ya musanta tuhumar da ake masa. Mai gabatar da kara ta ce laifin Salaudeen ya saba da sashe na 137 na kundin manyan laifuka na jihar Legas, wanda aka kirkira a shekarar 2015.
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

   Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta bayar da umarnin tsare wani limami da aka samu da laifin lalata da yarinya a Masallaci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });