Legit Hausa
Jami'an hukumar 'yan sandan jihar Kano sun bada sanarwar
mutuwar wani malamin makaranta, mai suna Femi Oguntumi dake zaune a unguwar
Dakata, wanda aka tabbatar da cewa ya kashe kanshi ne. Mutumin mai shekaru 40 a
duniya, wanda yake ma'aikaci ne a Kwalejin Karish, dake unguwar Kawaji, an iske
shi ya rataye kanshi a jikin rufin dakin shi.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, DSP Haruna
Abdullahi, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, ya ce yanzu haka
sun kai gawar marigayin asibitin Murtala domin gabatar da bincike akan shi. Ya
kara da cewa jami'an su sun fara gabatar da bincike akan dalilin da yasa Femi
ya rataye kanshi.
Ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari
na kisan kai ba, a lokuta da dama akan iske mutum ya sha guba ko ya rataye
kanshi, inda wasu suke alakanta hakan da yawan damuwa da kuma bakin talauci da
mutane ke fama dashi a wannan lokacin.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI