Kakakin majalisar Kano: Dan takarar gwamnati ya sha kaye


Legit Hausa

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun zabi Abdul'aziz Gafasa a matsayin sabon Kakakin majalisar jihar a karo na tara. Zaben ya biyo bayan sanar da fitowa takararsa da dan majalisar jam'iyyar PDP mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawan Hussain yayi jiya Litinin a lokacin da suka gabatar da zaman farko a dakin majalisar. 

Gafasa ya taba shugabantar majalisar jihar a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, a yanzu ya samu goyon bayan dukkanin mambobin jam'iyyar PDP su goma sha uku dake majalisar jihar. Majiya mai karfi ta bayyanawa jaridar Premium Times cewa, sauran mambobin jam'iyyar APC guda 18 sun zabi dan majalisa mai wakilatar karamar hukumar Doguwa. 

Hakan ya bai wa Gafasa damar samun kuri'u 21, yayin da shi kuma dan majalisa mai wakiltar Doguwa, wanda aka tabbatar da cewa shi gwamnatin jihar ke goyon baya ya samu kuri'u 18. Haka kuma an zabi dan majalisa mai wakilatar karamar hukumar Makoda, Hamisu Cigari, a matsayin mataimakin Kakakin majalisa a karo na hudu. 

Gafasa ya nuna farin cikinsa ga 'yan majalisar da zaben shi da suka yi, sannan kuma yayi alkawarin ba zai watsa musu kasa a ido ba. Ya kuma sha alwashin yin aiki da kowanne mamba na majalisar duk da cewa suna da bambancin jam'iyya da wasu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN