Legit Hausa
Sanata Omo-Agege na da kuri’u 68, yayinda Sanata Ekweremadu
na PDP ked a 37, sanata daya bai yi zabe ba, sannan an samu kuri’a mara kyau
guda daya. Sanata Omo-Agege ne kan gaba yayinda aka fara kirga kuri'un zaben
mataimakin shugaban majalisar dattawa.
An kammala shiri tsaf domin fara zaben wanda zai zamo
mataimakin shugaban majalisar dattawa na tara. Zababben sanatan Katsina ta
arewa Ahmad Babba- Kaita ya gabatar da sanata Ovie Omo-Agege a matsayin dan
takarar mataimakin Shugaban majalisar dattawa.
Zababben sanata mai wakiltan Enugu ta arewa, ya gabatar da
tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ga matsayin da ya
bari. Sanata Ekweremadu ya zagi Omo Agege a zauren majalisar dattawa, ya tuna
lamarin sace sandar iko a majalisar dattawa ta takwas.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi