Legit Hausa
Sanata Shehu Sani yayi martani ga jawabin Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari game da fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci cikin
shekaru 10. Sanatan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni ya bayyana cewa mutane na
bukatar a fitar dasu daga kangin ta’addanci kafin a fitar dasu daga kangin
talauci.
Hakazalika Sani ya bayyana cewa mutane na bukatar a ceto su
daga lamarin ta’addanci inda ya lissafa su a matsayin matsalar makiyaya, masu
garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe. Sanata Sani yace mutane na iya nema wa
kansu mafita daga talauci idan aka basu damar da za su iya fita gonakinsu cikin
kwanciyar hankali ba tare da tsoron hare-hare ba.
Ga yadda sanatan ya wallafa a shafinsa na twitter: “Kafin ka
fitar dasu daga kangin talauci ka fara fitar dasu daga kangin yan bindiga “A
yanzu mutanenmu kawai na so a fitar dasu daga kangin ta’addanci, makiyaya, masu
garkuwa da mutane da kashe-kashe; da kansu za su dauki matakin fita daga
talauci, da zaran sun fara samun ikon fita aiki a gonakinsu cikin kwanciyar
hankali.”
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu
Buhari yayi alkawarin fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci
zuwa ga tafarkin ci gaba a shekaru 10 masu zuwa. Buhari ya bayyana hakan ne a
jawabin bude taro a wajen bikin ranar 12 ga watan Yuni, wacce ta kasance ranar
bikin Damokradiyya a Abuja.
Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da
bunkasa tattalin arziki domin fitar da Najeriya daga talauci. Read more:
https://hausa.legit.ng/1243240-kafin-ka-fitar-da-yan-najeriya-daga-kangin-talauci-ka-fara-fitar-dasu-daga-kangin-yan-bindiga---shehu-sani.html
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI