Legit Hausa
Jaridar Forbes ta kasar Amurka ta saki jerin sunayen mutanen
da ta saba saki kowacce shekara na 'yan wasa guda dari da suka fi daukar
albashi mai tsoka a duniya, wanda da aka hada jimillar kudinsu ya kai dala
biliyan hudu a wannan shekarar, hakan yasa kudin wannan shekarar ya karu da
kashi biyar akan na shekarar da ta gabata.
Wanda ya fi kowa daukar kudi a jerin sunayen shine Lionel
Messi, wanda ya fito a na daya a cikin 'yan wasan da suka fi karbar albashi mai
yawa, hakan ya sa ya yiwa abokin hamayyarsa Christiano Ronaldo fintinkau.
Dan wasan dan kasar Argentina kuma dan kungiyar kwallon kafa
ta Barcelona ya samu 99.8 miliyan Pounds, inda shi kuma dan wasan kwallon kafa
na kungiyar Juventus Christiano Ronaldo ya samu 85.7 miliyan Pounds hakan ya
bashi damar fitowa a matsayin na biyu a jerin mutanen.
Na ukun su kuma shine dan wasan kwallon kafar nan na
kungiyar PSG Neymar, wanda ya samu 82.5 miliyan Pounds.
Ga jerin sunayen 'yan wasan guda 10 da kuma yawan kudaden da
suke dauka a kasa:
1. Lionel Messi - Kwallon kafa - Naira biliyan 45.9
2. Christiano Ronaldo - Kwallon kafa - Naira biliyan 39.5
3. Neymar - Kwallon kafa - Naira biliyan 38.1
4. Canelo Alvarez - Dambe - Naira biliyan 34
5. Roger Federer - Tennis - Naira biliyan 33.2
6. Russell Wilson - Football - Naira biliyan 32.1
7. Aaron Rodgers - Football - Naira biliyan 32
8. LeBron James - Kwallon kwando - Naira biliyan 32
9. Stephen Curry - Kwallon kwando - Naira biliyan 28.9
10. Kevin Durant - Kwallon kwando - Naira biliyan 23.4
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi