Jerin sunayen manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019


Legit Hausa

Wasan kwallon kafa na da mutukar muhimmanci a wurin al'umma, kuma akwai manyan 'yan wasan kwallon kafa na duniya da suke bin addinin Musulunci. Hakan ne ma yasa muka binciko muku wasu fitattun manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmai guda goma a wannan shekarar ta 2019. Ga jerin 'yan wasan a kasa:

1. Mohammed Salah (Egypt) Na farko a jerin shine Mohammed Salah, wanda aka fi sani da (Mo Salah), ko kokwanto babu dan wasan kwallon kafa na kungiyar Liverpool shine dan wasan da yafi kowa a cikinsu.

2. Fahad Al-Muwallad (Saudi Arabia) Al-Muwallad ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Levante, wacce ke buga wasan La Liga, bayan ya bar tsohuwar kungiyarsa ta Al-Ittihad. 

3. Mehdi Benatia (Morocco) Dan wasan mai shekaru 31 yana taka leda a kungiyar wasan kwallon kafa ta Juventus ne dake kasar Italy, bayan ya bar kungiyarsa ta Bayern Munich a shekarar 2017. 

4. Sardar Azmoun (Iran) Mutane da yawa basu san wannan dan wasan ba mai shekaru 23, saboda baya taka leda a yankin Turai. Sadar Azmoun yana taka leda ne a kungiyar wasa ta Rubin Kazan dake kasar Russia. 

5. Paul Pogba (France) Pogba ya bar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a shekarar 2012, inda ya tafi kungiyar Juventus, sannan ya kara dawowa Manchester a shekarar 2016 akan kudi fam miliyan 89.3. 

6. Ahmed Musa (Nigeria) Dan wasan Najeriyan ya yiwa kungiyar shi ta Najeriya kokari mutuka a wasan kwallon kafa da aka yi na duniya a shekarar 2018, a kasar Russia. 

7. Xherdan Shaqiri (Switzerland) Shaqiri dan asalin kasar Switzerland ne, kuma yayi wasanni masu yawa a kungiyoyin kwallon kafa na Turai. 

8. Mesut Ozil (Germany) Ozil wanda yake bugawa kasar Germany wasa, yayi murabus daga bugawa kasar wasa a shekarar 2014. Dan wasan Arsenal din, ya yiwa kungiyar tasa kokari matuka. 

9. Marouane Fellaini (Belgium) Yana da sauki a gano shi a cikin fili, saboda yanda yanayin gashinsa yake. Dan wasan mai shekaru 30 a duniya yayi suna a bangaren kungiyarsa dama kasar sa baki daya.
10. Sadio Mane (Senegal) Musulmin dan wasa na karshe a jerin shine Sadio Mane. Dan wasan 

kungiyar kwallon kafa ta Liverpool yana wasa tare da takwaransa, Mohammed Salah. Shi da Salah suna buga wasa fiye da tunanin mutum idan suka hadu. Wannan mun tsakuro muku kadan daga cikin 'yan wasan kwallon kafa Musulmi ne, akwai su bila adadin
 

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN