Jerin sunaye: Gwamnatin tarayya ta kwace rijiyoyin man fetur 6


Legit Hausa

Sashen kula da albarkatun man fetur (DPR) ya kwace lasisin hakar man fetur (OML) da kuma wani lasisin na hakar man fetur mai karamar daraja (OPL) daga hannun wasu kamfanoni guda biyar. 

A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, DPR ta bayyana cewar ta kwace lasisin ne bisa umarnin shugaban kasa. Ta ce an kwace lasisin ne saboda tarin bashin da ake bin kamfanonin da suka mallaki rijiyoyin man fetur din. 

Kamafnonin biyar da abin ya shafa su ne; Pan Oil Corporation (OML), Allied Energy Resources Nigeria (OML 120 da 121), Express Petroleum and Gas Company (OML 108), Cavendish Petroleum Nigeria (OLL 110) da Summit Oil International (OPL 206).
 

 DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN