Jawabai 9 da Buhari yayi a ranar dimokuradiyyaLegit Hausa

A ranar Laraba 12 ga watan Yuni, aka gudanar da bikin ranar dimokuradiyar Najeriya bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sauya ranar da a baya aka saba gudanar da bikin ta a 29, ga watan Mayu.

Shugaban kasa Buhari ya gabatar da jawabai da dama musamman inda alkiblar gwamnatin sa a wa'adi na biyu za ta fuskanta da kuma wurare da sabuwar gwamnatin sa za ta mayar da hankali a kai. Mun kawo mu wasu jerin muhimman jawabai da shugaban kasar ya gabatar yayin bikin ranar dimokuradiyya da aka gudanar a dandalin Eagle Square na garin Abuja.

1. Ina mutunta harkokin gudanar wa na hukumar INEC Shugaban kasa Buhari ya ce ba zai gushe ba wajen ci gaba da ganin kimar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC a sakamakon bajintar da nuna wajen tabbatar da zaben nagari da ya tsarkaka daga duk wani nau'i na rashin gaskiya. 

2. Ina godiya da samun goyon bayan na zabe na a matsayin shugaban kasa karo na biyu Shugaban kasa Buhari ya kwarara yabo gami da godiya ga dukkanin wadanda suka bayar da gudunmuwa wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar sa ta APC. Ya yi godiya ta musamman a kan wadanda ba gushe ba wajen jefa masa kuri'a tun daga zaben 2003 kawowa yanzu. 

3. Najeriya babbar kasa ce a duniya Buhari ya ce kasar Najeriya tana gogayyar kafadar ta da wasu kasashen duniya inda alkalumman majalisar dinkin duniya a kwana kwanan suka tabbatar da cewa akwai yiwuwar adadin al'ummar kasar nan zai kai kimanin miliyan 411 daga yanzu zuwa shekarar 2050. Najeriya za ta kasance a mataki na uku ta fuskar yawan al'umma bayan kasar Sin da kuma Indiya. 

4. Najeriya ta ciri tuta a nahiyyar Afirka Buhari ya ce kasar Najeriya ta ja ragama tare da rataya nauyin wanzar da zaman lafiya musamman a kasashen dake makotaka da ita a nahiyyar Afirka. Ya bayar da misalin kasashen Gambia, Zimbabwe, Mozambique, Namibia da kuma kasar Afirka ta Kudu.

5. Dole ne mu inganta hanyoyin sufuri na ruwa, titi, layin dogo da kuma wutar lantarki a zamance A yayin da gwamnatin sa ta sha alwashin ribatar dukiyar sa wajen bunkasa ci gaban kasa, Buhari ya ce akwai muhimmiyar bukata ta inganta gine-ginen tituna, layin dogo, tashohin jiragen ruwa da na sama da kuma wutar lantarki a zamanance. 

6. Ba ni da wani buri face sadaukar da rayuwa ta wajen yiwa Najeriya hidima Shugaban kasa Buhari ya ce ya shafe tsawon rayuwar sa wajen yiwa Najeriya hidima tun bayan da mallaki hankalin kansa. Ya lissafa lunguna da sakonni na kasar nan da ya yiwa Najeriya bauta da suka hadar da Kaduna, Legas, Abeokuta, Makurdi, Fatakwal, Maiduguri, Ibadan, Jos da kuma Abuja. 

7. Masu adawa ne kadai ke tantamar ci gaban da Najeriya ta samu a gwamnati na Sabanin kalubale da kasar nan ta fuskanta na matsin tattalin arziki da kuma rashin tsaro, Buhari ya ce gwamnatin sa babu ko shakka ta taka rawar gani wajen samun nasarori da suka tabbatar da ci gaba a kasar nan. 

8. Matukar kasar Sin da Indiya na ganin karan su ya kai tsaiko a fagen ci gaba, ba za a bar Najeriya a baya ba Shugaban kasa Buhari ya ce sabanin kalubale da kasar Indiya da kuma Sin suka fuskanta, a halin yanzu sun kasance kan sahu na gaba cikin jerin kasashen duniya masu bugun gaba da samun ci gaba. Ya ce hakan kuwa za ta kasance ga kasar Najeriya domin kuwa ba za ta zamo koma baya ba.

9. Ina alfahari da kananan masana'antu da kuma kananan 'yan kasuwa Shugaban kasa Buhari yace yana matukar alfahari da kananan 'yan kasuwa da kuma masana'antu masu wadatar da kasar nan da har a wani sa'ilin ake fitar da kayayyakin su zuwa kasashen ketare. Ya ce hakan yana bunkasa tattalin arzikin kasar nan ba kadan ba. 


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN