Ina daukan nauyin mata na 3 da yara 11 daga garkuwa da mutane - Sani Ibrahim

Legit Hausa

wata magarkama da babban sifeton 'yan sanda na kasa (IGP) ya sa aka ware domin ajiye masu garkuwa da mutane da aka kamo daga sassan kasar nan.
A ganawar da wakilin jardar ya yi da masu garkuwa da mutanen, wani daga cikinsu mai shekaru 45 a duniya ya bayyana cewar yana da mata uku da yara 11 wadanda yake daukar nauyi daga muguwar sana'ar da ya ke yi.
Mutumin mai suna Sani Ibrahim, wanda aka fi sani da Kwalba saboda shan giya, ya bayyana cewar garkuwa da mutane ta yi masa rana domin ya samu kudi fiye da wadanda ya samu lokacin da ya fara sata kafin daga bisani ya koma fashi da satar shanu.
A cewarsa, aikin ta'addanci ya biya shi saboda da irin kudin da ya samu daga aikata laifuka ne ya auri mata uku da suka haifa masa yara 11. Sannan ya kara da cewa koda yaushe yana cikin kudi, lamarin da ya sa giya da mata basa yanke masa.
Da yake bayar da labarin yadda ya zama mai garkuwa da mutane, Ibrahim ya bayyana cewa: "na fara garkuwa da mutane ne a kan wani mutum da ya samu sabani da yaro na. Mun yaudare shi tare da tsare shi a tare da mu har sai da mutanensa suka kawo mana N400,000 kafin mu sake shi."
Daga wannan lokaci ne idon Ibrahim ya bude da garkuwa da mutane har ta kai ga ya bar sauran aiyukan ta'addanci da ya ke aikata wa tare da koma wa yin garkuwa da mutane kawai.
Kazalika ya bayyana cewa daga nan ne ya shiga harkar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa har zuwa lokacin da ya hadu da Buharin daji, wani gawurtaccen dan bindiga da aka kashe a jihar Zamfara.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN