Legit Hausa
Mayakan Boko Haram sun kai hari bataliyar soji ta 158 dake
kauyen Kareto na karamar hukumar Mobbar dake jihar Borno inda suka kashe
kwamandan bataliyar da jami’ai da dama. Kakakin hukumar sojin Najeriya, Kanal
Sagir Musa bai samu damar amsa rubataccen sakon da yan jarida suka aika masa
kan lamarin ba a ranar Juma’a.
Akwai fargaban cewa har yanzu yan ta’addan na nan a
tsakankanin karamar hukumar inda suke sake shirin kai wasu sabbin hare-hare ga
dakarun soji da jama’ar gari. Harin da aka kai bataliya ta 158 wanda yayi
sanadiyar kisan kwamanda bataliyar yazo ne bayan wata daya da aka dasa bam a
bataliya ta 154 wanda yayi sanadiyar mutuwan kwamandanta Laftanal Kanal Yusuf
Aminu.
Kwamandan tare da dakarun soji biyu sun rasa rayukansu ne
sakamakon fashewar bam a ranar 13 ga watan Mayun 2019, lamarin da hukumar sojin
Najeriya ta tabbatar da aukuwarsa har ma Hafsun soji ya halarci jana’izarsu.
Wakilin jaridar punch ya ruwaito ranar Juma’a cewa: “ Mayakan Boko Haram sun
kai hari a bataliyar soji ta 158 a ranar dimokuradiyya inda suka sace
kayayyakin sojin sukayi awon gaba dasu.”
Kwamandan bataliyar wanda har yanzu ba’a tabbatar da
haqiqanin sunansa ba, an shaida mutuwarsa tare da sojoji da dama. Wata majiya
daga bangaren sojin ta ce: “ Gaba daya dakarunmu dake wannan karamar hukumar
basu da karfin fada da yan ta’addan, muna bukatar karin karfi da makamai ta
yadda zamu iya fuskantar abokan gaba.”
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi