Legit Hausa
Ganyen Kabeji na daya daga cikin kayan lambu da mutane ke
yawan amfani dashi, musamman a cikin abinci ko kuma kwadon shi da kuli.
Da yawan mutane suna cin wannan ganye ne don marmari ba tare
da sun san tarin alfanu da yake dashi ba wajen magance wasu cututtuka a jikin
dan Adam. Kabeji na dauke da sinadarin ‘Protein’ wanda ke gina jiki, da kuma
'Vitamin C' wanda ke warkar da cututtuka a jiki dan Adam.
Ga hanyoyi 5 da za a iya amfani da wannan ganye wajen
magance wasu manyan cututtuka
1. Ganyen Kabeji na kashe kwayoyin cuta da ke shiga cikin
budadden ciwo: Za a daddaka ganyen sai a murza a saman ciwon. Yin haka na
taimakawa matuka wajen kashe kwayoyin cuta da ka iya shiga cikin ciwon.
2. Kabeji na warkar da ciwon nono da tsayar da ruwan nono ga
macen da ta gama shayarwa: Ga matan da suka cire ‘ya’yansu daga bakin nono,
ganyen kabeji na taimakawa wajen hana ciwon nono ya kuma hana zuban ruwansa
bayan yaye. Mace za ta dauki ganyen ta lullube nononta da shi da daddare sannan
ta cire ganyen washe gari.
3. Kabeji na maganin gyambon ciki: Ga mutummai fama da
atsalar gyambon ciki , sai ya lazmci cin ganyan kabeji danye wanda aka yi
kwadon shi da kuli ko kuma dafaffe a cikin shinkafa ko fate ko kuma ya sharuwan
ganyen kabejin.
4. Kabeji na hana saurin tsufa: Yawan cin kabeji ko kuma
wanke fuska a ruwansa na hana tsufa da wuri.
5. Ganyen Kabeji nakawar da ciwon kai: Kafin a kwanta da
daddare sai a tsinki ganyen kabeji a lullube kai da shi. Yin haka zai hana
ciwon kan da ake ji.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi