Legit Hausa
Rikicin jam’iyyar APC a ranar Asabar 22 ga watan Yuni, 2019
ya sake daukar wani sabon salon yayin da gwamnonin jam’iyyar ke neman wanda zai
maye masu gurbin shugaban jam’iyyar na qasa Adams Oshiomole.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa akwai kishin-kishin
din tumbuke shi daga sakateriyar jam’iyyar ta qasa a daidai lokacin da yake daf
da cika shekar guda a matsayinsa na shugaban jam’iyyar. Rahatonni da dama sun
sake tabbatar mana da cewa gwamnonin APC sun nemi sabon shugabanci na jam’iyyar
yayin da suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari a ckin makon da ya gabata.
Haka zalika majiyar da ta sanar damu wannan labarin ta ce,
shugaban gwamnonin APC Atiku Bagudu na jihar Kebbi shi ne ya jagoranci
gwamnonin zuwa wurin wannan ganawa da suka yi da shugaban qasa. Bugu da kari
majiyar ta cigaba da cewa, akwai yiwuwar za’a kira zama na musamman domin
sasanta Oshiomole da mataimakinsa. Zaman wanda ake sa ran zai kunshi majalisar
gwamnoni da kuma majalisar zartarwa ta APC.
Yayin da ake maganar wanda zai maye gurbin kujerar tsohon
gwamnan Edon in har gwamnonin sunyi nasarar tumbuke shi, ga abinda majiyar ke
cewa: “ Gwamnoni na neman wanda zai maye gurbin shugaban jam’iyyar APC.
Dukkanin tunaninsu ya tattara ne a bangaren kudu maso kudu, ba su kallon kudu
maso yamma ko kuma kudu maso gabas wadanda su ne marasa yawa cikin jam'iyyar.”
Tun a kwanan baya dai dangantaka ta riga tayi tsami tsakanin
Shuaibu Lawal mataimakin Oshiomole na yankin Arewa da shi kansa shugaban
jam'iyyar APC na qasa. Inda Shuaibu ke zarginsa da tarwatsa jam'iyyar ta su ta
hanyar rarraba kawunan 'yan 'yan jam'iyyar.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
SIYASA