Legit Hausa
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Muhammad Bala Abdulkadir ya
bayyana damuwarsa akan rikicin da ke faruwa tsakain Sarkin Kano Muhammad Sanusi
II da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje. Gwamnan ya sha alwashin jagorantar
wata tawaga domin kawo sasanci a kan lamarin.
Gwamnan wanda ke rike da sarautar Kauran Bauchi, ya bayyana
hakan ne a yayinda tawagar Sarki Sanusi karkashin jagorancin Makaman Kano,
Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, suka kai masa ziyarar taya murna akan zama
gwamnan jihar Bauchi da yayi.
Sanata Bala ya nuna mtukar damuwa, inda ya bayyana rikicin a
matsayin koma-baya ga ci gaban yankin arewaacin kasar da ma Najeriya baki daya.
Gwamnan ya ja hankalin takwarorinsa gwamnoni da su tsame kansu cikin siyasantar
da sha’anin Sarauta, yana mai bayyana cewar Sarakuna suna da cikakken ikonsu da
martabarsu wajen gina kasa da al’ummar kasa.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata
kotu da ke zama a Kano a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni ta dage sauraron karar
da mahukuntan fadar jihar suka shigar akan Gwamna Umar Ganduje da wasu mutane
bakwai.
Mahukunta hudu na fadar Kano, Yusuf Nabahani (Madakin Kano),
Abdullahi Sarki Ibrahim (Makaman Kano), Bello Abubakar (Sarkin Dawakin Mai
tuta) da Muktar Adnan (Sarkin Mai Kano), sun shigar da karar Kakakin majalisar
dokokin Kano, Gwamnan jihar Kano, Babban alkali , Tafida Abubakar Ila, Ibrahim
A Gaya, Ibrahim Abubakar II da Aminu Ado Bayero bisa kafa sabbin masarautu da
nada sarakuna.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi