Fitaccen Malami Sheikh Gummi ya bukaci Buhari ya gaggauta sakin Dasuki da Zakzaky


Legit Hausa

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki Sambo Dasuki, tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Goodluck Jonathan, ba tare da wani bata lokaci ba. Kazalika, Malamin ya yi wani kira ga gwamnatin a kan ta saki shugaban mabiya kungiyar shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky. 

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne ranar Asabar yayin rufe karatun tafsirin watan azumin Ramadana a masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna. Ya ce akwai bukatar gwamnati take yi wa umarnin biyayya.

 Gumi ya kara da cewa babu dalilin cigaba da tsare mutanen biyu tunda tuni ta bayar umarnin a sake su. Ya ce zai fi sauki ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da Sheikh Zakzaky a kan cigaba da tsare shi a kurkuku.

 "A nan gida Najeriya, ina son yin kira ga gwamnati da ta kara duba lamarin Kanal Sambo Dasuki domin a sako shi ba tare da bata lokaci ba, haka ma shugaban 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
"Su sake shi idan ya so sai su tattauna da shi domin su fuskanci juna. Ba daidai bane gwamnatin ta ki yin biyayya ga umarnin kotu. 

"Matukar gwamnati ba ta yi biyayya ga doka ba, dole a samu haramtattun kungiyoyi da zasu ke taka doka da gangan. Babu wani uzurin aikata ta'addanci. "Dole gwamnati ta nuna kyakyawan misali ta hanyar sakin su, musamman kanal Sambo Dasuki," a cewar sa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN