Fadar shugaban kasa tayi martani kan zanga-zangar neman koran na hannun daman Buhari


Legit Hausa

A daren jiya Litinin ne fadar shugaban kasa tayi martani kan zanga-zangar da kungiyar 'Concerned APC National Stakeholders' (CANS) su kayi na neman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami wasu daga cikin na hannun damansa da wasu ke zargin su ke juya akalalar kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce wasu ne suka nauki nauyin masu yin zanga-zangar. "Za ku cigaba da ganin wasu zanga-zangar da wasu za su dauki nauyin yin. A cikin wata otel da ke babban birnin tarayya Abuja, akwai shagon masu shirya zanga-zanga. Idan kana da kudi, za su rubuta maka jawabin zanga-zangar, su baka takardu da mutane maza da mata har ma da jagorar zanga-zangar wanda mafi lokaci lauya ne.

"Saboda haka ba muyi mamaki ba. Nan ba da dadewa ba, 'yan jarida da masu daukan hotuna za su fara daukan hayan masu wannan zangan-zangan domin musgunawa masu tace labarau da basu kauna. "Abin lura a nan shine Shugaban kasa ba mutum ba ne da irin wannan yaudarar.

Yana da tsare-tsaren sa kuma shi kadai zai zabi wadanda ya ke son ya yi aiki tare da su da kuma wadanda zai kora. Maganan gaskiya shine wannan zanga-zangan ba za ta zanja komai ba," inji shi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN