Duk da rashin zabensa, Abu Najakku ya yi wa jama'ar Bunza wani babban alhairi

Tsohon dan takarar kujerar Majalisa na tarayya mai wakiltar Birnin kebbi , Kalgo da Bunza a jihar Kebbi, Hon Abubakar Najakku watau Abu Najakku ya cika alkawari da ya dauka wa jama'ar Bunza a lokacin yakin neman zabe ta hanyar bayar da tsabar kudi har Naira dubu dari biyar cur N500.000 ta hannun wani kwamiti wanda Hon Aliyu Bunza ya karba ranar Talata 5 ga watan Yuni, 2019.

A jawabinsa a dakin da aka zauna lokacin ziyararsa a garin Bunza, Kodineta na yakin neman zabe na Hon. Abu Najakku watau Hon Bello Sani ya ce "Hon Abu Najakku ya dau alkawari lokacin yakin neman zabe a garin Bunza cewa ko mutanen Bunza sun zabe shi ko basu zabe shi ba zai zo ya bayar da tallafin N500.000 domin a taimaki Marayu da marasa lafiya. Shi ne Allah ya sa muka zo domin cika wannan alkawari".

Bello Sani ya daga kudin ya ce ga kudin mu zo da su " Yanzu za mu hanunnta su ga kwamiti wanda zasu yi wannan aiki a kowane Ward, Kowane Ward zai sami Naira dubu ashirin da biyar N25.000, gida biyar ko marasa lafiya biyar kowa zai sami N5000. Hakazalika za a ba Makabarta N40.000 domin gyara, daga bisani zamu je Asibitin Bunza domin mu mika tallafin shan magani N5000 da abinci ga kowane mara lafiya da ke kwance a gadon Asibiti. Akwai kuma wajen da aka bukaci ayi Rijiya, za mu je tare da Hon. Abu Najakku domin a gan wajen kuma za a yi wannan Rijiya".

Idan baku manta ba, a kwanakin karshe na watan Ramadana, mun kawo maku labarin yadda Hon. Abu Najakku ya yantar da wasu Fursunoni daga gidan Kurkukun Birnin kebbi bayan ya biya masu Tara da Koto ta yanke masu.

Tsohon dan takarar kujerar Majalisar dokoki na jihar Kebbi mai wakiltar Bunza, Hon Aliyu Bunza, a nasa jawabin, ya ce, " Wannan ya zama abin koyi ga sauran yan siyasa, duk da yake Hon Najakku ba dan Bunza bane, amma ya fara wannan aikin alhairi daga garin Bunza duk da yake Allah bai kaddari ya ci zaben fitar da gwani ba, amma sai ga shi ya saka wa mutanen Bunza da alhairin"

Haj. Zuwaira Umaru,  Murtala Bello, Altine Bala Tudun wada Birnin kebbi, da Umaru Giwa Raha sun yi kyakkyawan jawabi tare da nuni bisa alhairi, kuma suka yi jawabai daban daban bisa yadda suka fahimci tsarin harkar siyasar Hon. Abu Najakku, kuma suka ayi kyakkyawar addu'a daga karshe.

A nasa jawabi, Hon. Abu Najakku, ya ce "  Sunana Abu Najakku, za ku iya tunawa a lokacin yakin neman zabe, na yi maku alkawari a wannan daki cewa ko an zabe ni ko ba a zabe ni ba zan zo nan in aje zunzurutun kudi har rabin Miliyan N500.000 domin tallafa ma jama'a. Idan za ku iya tunawa, na gaya maku cewa ni na fito wannan harka ne domin in yi wa jama'a hidima. Ina son in gaya maku cewa zunzurutun kudin nan da na zo da su a yau har N500.000 naira na gugan naira halaliya na ne babu haramun ko sisi a ciki".

"Abin da ya sa na dawo nan domin in cika maku alkawari shine, ina son ku sani akwai yan siyasa kuma akwai yan siyasa, ni siyasa da na zo da ita siyasa ce ta tsakani na ne da Allah kuma da jama'a, siyasa ce ta ci gaba, siyasa ce ta yi ma jama'a hidima, siyasa ce ta in hana kaina in ba jama'a da suka fi ni bikata".

Tawagar Najakku ta zarce zuwa babban Asibitin Bunza, inda ya ba kowane mara lafiya da ke kwance a gadon Asibiti tallafin Naira dubu biyar N5000 domin su sayi magani.

Daga karshe ya ziyarci Makarantar Alkur'ani na Malam Altine Bajifa, kuma ya alkawarta cewa zai yi masu Borehole, watau rijiyar burtsatse bisa roko da suka yi domin a taimaka masu.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN