Dubu ta cika: An kama wani soja da yake sayarwa da 'yan ta'adda makamai a jihar Kaduna

Legit Hausa
An kama wani soja dan shekara 32 mai suna Corporal Koza Yabiliok, a jihar Kaduna da laifin sayar da alburusai ga wasu wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suke addabar mutanen yankin shekara da shekaru.
Da aka bincike shi, Yabiliok ya bayyanawa manema labarai cewa yana sayar da kowanne harsashi guda daya akan kudi naira dari hudu (400). Sojan yana aiki a garin Jaji dake jihar ta Kaduna.
Yabiliok ya bayyana cewa bai taba tunanin cewa abokin kasuwancin nasa dan garkuwa da mutane bane. Ya kara da cewa dan ta'addar kawai ya sanar dashi cewa yana amfani da harsashin domin kare kanshi daga barayin shanu ne. "Haka ne yasa nake siyar mishi da harsashin ban san cewa shi mai garkuwa da mutane ba ne," in ji shi.
A lokacin da yake magana da manema labarai, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ali Aji-Janga, ya ce sun samu nasarar kama mutane 61 da suke da laifuka kala-kala da suka hada da, garkuwa da mutane, fashi da makami, kissan kai da kuma satar shanu. Ya ce sun kuma samu nasarar kwace muggan makamai, harsashi, kwayoyi, da ababen hawa daga wajen 'yan ta'addar.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN