Legit
Hausa
Gab da
karewar wa'adinsa matsayin gwamnan jihar Osun, Ibikunle Amosun, ya tuntubi
kwamishanan yan sandan jihar, Bashir Makama, domin bayyana masa cewa yana da
dubunnan bindigogi da miliyoyin harsasai da ya boye a gidan gwamnati.
Ya kira
kwamishanan yan sandan ne domin mika masa bindigogin tun da yanzu zai bar gidan
gwamnati kuma abokin hamayyarsa ne zai gaje sa. Wanda gwamna Amosun yaso yaci
zabe, Adekunle Akinlade, na jam'iyyar APM ya sha kayi a hannun gwamna na yanzu,
Dapo Abiodun, na APC wanda ya laburta cewa magabacinsa bai bar ko sisi a asusun
gwamnatin jihar ba. Bayan ganawar Amosun da kwamishanan yan sanda, Makama tare
da wasu jami'an yan sanda suka kwashe dubunnan makamai da harsasan da gwamnan
ya boye.
Daga cikin
abubuwan da aka tarar sune bindigogi kirar AK47 guda 1000, carbin harsasai
milyan hudu, rigar kare harshashi 1000, da motar mara jin harsasai. A lokacin
mika makaman, Amosun ya ce an siya wadannan makamai ne domin kare al'ummar
jihar kuma ya yanke shawarar ajiyesu a gidan gwamnati saboda yana tsoron abinda
jami'an tsaro za suyi da shi idan aka basu Daga baya aka kai makaman hedkwatan
hukumar yan sanda dake Elewe-Eran, Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun. Makonni
hudu bayan haka, manyan jami'an tsaron Najeriya sun mamakin ta yaya gwamnan
farin hula zai ajiye dubunnan makamai a gidan gwamnati.
Suna
mamakin shin me yasa har yanzu ba'a damke gwamna Amosun ba saboda abinda yayi
ya sabawa dokar kasa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
TSARO