Legit Hausa
An samu kwararan shaidu dake nuna yadda aka dinga rabawa
tsofaffin 'yan majalisar dokoki da sababbi kudi domin su zabi Femi Gbajabiamila
a matsayin Kakakin majalisar wakilai ta kasa.
Jaridar Sahara Reporters ta
tabbatar da cewa an bai wa kowanne dan majalisa katin cire kudi, wanda aka
sanya kudi masu tarin yawa a cikin kowanne, domin jawo hankalin su wurin zabar
dan majalisar.
Duk da dai jaridar tace ba za ta iya saurin yanke hukunci
akan ko nawa ne a cikin kowanne kati ba, amma tana da tabbacin cewa akwai
makudan kudade a ciki.
An raba katin ga wadanda tun farko suka nuna goyon bayansu
ga Gbajabiamila, sannan kuma suka nuna suna tare dashi a kowanne hali. Kafin a
fara gabatar da zaben Kakakin majalisar, an hango da yawa daga cikin 'yan
majalisar a bangaren bandakin maza na majalisar suna raba daloli ga junansu.
Idan ba manta ba kimanin 'yan majalisar tarayya 66 ne suka zabi Sanata Ahmad
Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa, kuma anyi zargin cewa an bai wa
kowannen su naira miliyan 25 domin su zabe shi.
Gbajabiamila ya lashe
zaben Kakakin majalisar da kuri'u 281, yayin da abokin hamayyarsa Umar Bago ya
samu kuri'u 78.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI