Budurwa mai riko da addini ta fita da sakamako da ya fi na kowa a Jami'a


Legig Hausa

Labari ya iso gare mu cewa a na ta faman murna da farin ciki a jami’ar tarayya da ke Abuja watau UNIMAID bayan da wata Baiwar Allah ta kammala karatu a matsayin gwarzon wannan shekarar. Wata ‘Daliba da ta kammala karatu daga sashen kimiyya ita ce ta ciri tuta a zangon karatu na bana inda ta kare jami’ar ta Abuja da maki 4.82.

Sunan wannan Baiwar Allah Talatu Adamu. Kamar yadda wani Matashi wanda ya ke jami’ar mai suna Abdulhameed Nuhu Omeiza (wanda ake fi sani da Abu Jandal) ya sanar, Talatu ita ce gwarzon UNIABUJA na shekarar 2018/19. A kwanan nan ne jami’ar ta yaye ‘Daliban da su ka kammala karatu a biki na 23 da aka shirya. Talatu ta na cikin jami’n kungiyar MSSN na Musulunci da ke wannan jami’a da ake ji da ita.

 Malam Abdulhameed Nuhu Omeiza ya ke cewa nasarar da Talatu ta samu ya nuna cewa akwai riba wajen riko da addini da kuma dagewa da kwazo da bada himma wajen neman abin Duniya. Kwanakin baya ne kuma aka samu wani Matashi mai suna Nuhu Ibrahim wanda ya doke duk wani tarihi da aka kafa a jami’ar ABU ta Zariya inda ya kammala Digirinsa da maki 4.94.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN